Isa ga babban shafi
Najeriya-Faransa

Ina sauraren sashen Hausa na RFI- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa takwaransa na Faransa Emmanuel Macron cewa, yana sauraren labarai da rahotanni da hirarrakin da sashen Hausa na RFI ke watsawa a duk rana.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ta takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari a Abuja
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ta takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari a Abuja Présidence du Nigéria /Reuters
Talla

Buhari ya shaida wa Macron haka ne a yayin wata ganawar keke da keke da ta gudana a tsakaninsu a birnin Abuja.

Macron wanda ya kammala ziyarar kwanaki biyu a Najeriya, ya jinjina wa kwazon RFI Hausa wajen yada labaran duniya ga al’umma daban-daban a sassan duniya musamman a nahiyar Afrika.

“Abu ne mai kyau a samu kyakkyawar mu’amala tsakanin harshen Faransanci da sauran harsunan Afrika, musamman ma harshen Hausa, ina jinjina ma ku sosai lura da irin gagarumin aikin da sashen Hausa na RFI ke gudanarwa.” In ji Macron.

Shugaban ya kara da cewa, “ Wannan alama ce da ke kara tabbatar da cewa abu ne mai kyau a samu irin wannan musaya ta al’adu da kuma harsuna. Shugaba Buhari da kansa ya ce, lokuta da dama yana sauraren sashen Hausa na RFI."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.