Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaban Faransa ya jinjinawa sashin Hausa na RFI

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya jinjinawa ma’aikatan sashin Hausa na Radio France Internationale, dangane da jajaircewarsu wajen gudanar da aiki cikin kwarewa da tsanaki.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayin jawabi ga matasa da masu ruwa da tsaki kan harkar kasuwanci da bunkasa kanana da manyan masana'antu a Eko Hotels da ke birnin Legas.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayin jawabi ga matasa da masu ruwa da tsaki kan harkar kasuwanci da bunkasa kanana da manyan masana'antu a Eko Hotels da ke birnin Legas. REUTERS/Akinunde Akinleye
Talla

Macron ya bayyana haka ne a birnin Legas, a yau Laraba, rana ta biyu, kuma ta karshe a ziyarar da shugaban ya kai tarayyar Najeriya.

Yayin zantawa da AbdoulKareem Ibrahim Shikal na RFI Hausa, a cibiyar yada al’adun kasar Faransa da ke birnin na Legas a Najeriya, Emmanuel Macron ya ce, ya ce yana da muhimmanci ainun a samu kyakkyawar mu’amala tsakanin harshen Faransanci da sauran harsunan Afirka, musamman ma harshen Hausa, inda ya yaba da irin gagarumin aikin da ya ce sashin Hausa na RFI ke gudanarwa.

Shugaba Macron ya kara da mika sakon zumunci ga ilahirin masu sauraren RFI Hausa, harshen da ya bayyana shi a matsayin mai matukar muhimmanci.

Zalika shugaban na Faransa ya ce yana sane da irin matsalolin da ke ci wa al’ummar wannan yanki tuwo a kwarya, da suka hada da talauci da kuma mafin munin ayyukan ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.