Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai ziyarci Filato don jajanta wa jama'ar jihar

Rahotanni daga Najeriya na cewa akwai yiwuwar shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Filato a yau Talata don jajanta wa al’ummarta sakamakon rikicin baya-bayan nan da ya lakume rayukan mutane kusan 100.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mukarrabansa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mukarrabansa REUTERS/Tiksa Negeri/File Photo
Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta rawaito cewa, shugaba Buhari zai yada zango a Filato bayan ya baro birnin Calabar da ke jihar Cross Rivers a yammacin yau.

A wannan safiya ne shugaba Buhari ya kama hanyarsa ta zuwa Calabar daga birnin Abuja don kaddamar da wasu ayyukan gwamnati a jihar.

A jiya ne mataimakin shugaban, Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci Filato saboda wannan ibtila’in da ya afka ma ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.