Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 86 sun mutu a rikicin jihar Filato

Hukumomin tsaro a jihar Filato da ke Najeriya sun tabbatar da kashe mutane 86 sakamakon wani tahsin hankalin da ya barke a karamar hukumar Barikin Ladi, kana ya kuma fantsama zuwa wasu kananan hukumomi biyu.

Jihar Filato ya yi fama da munanan tashe-tashen hankula a can baya, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama
Jihar Filato ya yi fama da munanan tashe-tashen hankula a can baya, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama Photo : Pius Utomi Ekpei/AFP
Talla

Bayanan da ke fitowa daga jihar sun ce, an kwashe kwanaki ana dauki ba dadi tsakanin Fulani makiyaya da manoma 'yan kabilar Berom a yankin da ya dade ya na fama da tashin hankali.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Undie Adie ya ce, binciken da suka gudanar ya tabbatar musu da samun gawarwaki 86 da aka kashe tsakanin bangarorin biyu, yayin da aka raunana mutane 6, kana aka kona gidaje 50.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya ce, wannan ya sa matasa 'yan kabilar Berom tare mutane a hanyar Jos zuwa Abuja, in da suka rika kai hari kan matafiyan da aka fahimci suna da alaka da Hausa-Fulani, abin da ya sa wasu suka sha da kyar, yayin da aka hallaka wasu, kana aka kona motocinsu.

Wannan ya sa gwamnan Filato, Simon Lalong kiran taron gaggawa na majalisar tsaro da kuma kafa dokar hana fita a kananan hukumomin Barikin Ladi da Riyom da kuma Jos ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.