Isa ga babban shafi
Najeriya

Makarfi ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugabancin Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, kuma tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Sanata Ahmed Makarfi, ya bayyana aniyarsa ta neman tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben 2019.

Tsohon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Ahmed Makarfi, yayin gaisawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Tsohon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Ahmed Makarfi, yayin gaisawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. FEMI ADESINA
Talla

Makarfi ya sanar da shawarar da yanke ne, yayin zantawa da manema labarai a garin Kaduna a ranar Lahadi.

Tsohon gwamnan jihar ta Kaduna, ya ce, ya yanke shawarar neman takarar shugabancin Najeriya ce, bayan da ya nemi jin ra’ayoyin muhimman mutane da ke sassan kasar, tun bayan sauka daga mukamin shugaban jam’iyyar adawa ta PDP.

A cewar Makarfi tun daga lokacin zuwa yanzu, ra’ayoyin da ya ke cin karo da su yayin neman shawarwari, na ci gaba da kara mishi kwarin gwiwar bayyana aniyarsa.

Dangane da tsokacinsa kan gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kuwa, Makarfi ya ce tilas a yabawa kokarinta wajen yakar ta’addanci, musamman murkushe mayakan Boko Haram, sai dai tsohon gwamnan, ya ce nasarar samar da tsaro a kasar zata fi karfi da ace, ma’aikatun masu alhakin tabbatar da tsaron na aiki tare kamar yadda ya kamata.

A bangaren yaki da cin hanci da rashawa kuma, Ahmed Makarfi ya ce akwai rauni, la’akari da cewa ana zabar wadanda ake gurfanarwa ne ko bincikarsu bisa zargin sace dukiyar jama’a.

Zuwa yanzu dai a fagen siyasar Najeriyar, a karkashin jami’iyyar adawa ta PDP mutane 5 ne suka bayyana aniyar neman takarar shugabancin kasar.

Mutanen sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau, gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo da kuma tsohon ministan ayyuka na musamman a gwamnatin da ta shude Tanimu Turaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.