Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Barista Aliyu Zaria kan murabus din gwamnan Zamfara daga mukamin shugaban jami'an tsaro

Wallafawa ranar:

Gwamnan jihar Zamfara a tarayyar Najeriya Abdulaziz Yari, sanar da ya sanar da yin murabus daga mukamin shugaban jam’ian tsaron jihar, la’akari da yadda har yanzu jami’an tsaro suka kasa kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar.Yayin da ya ke shaidawa manema labarai matakin da ya dauka a jiya a Talata Mafara, gwamna Yari ya ce hakan ya zama tilas, domin bashi da ikon sarrafa jami’an tsaron da ke kokarin shawo kan hare-haren ‘yan bindiga da ake ci gaba da samu a jihar ta Zamfara.Matakin na gwamnan jihar ta Zamfara, ya zo ne kwanaki kalilan, bayan da ya ya bukaci majalisun tarayyar Najeriya su cire wa gwamnoni mukamin da aka lakaba musu na shugabannin jami’an tsaron jihohinsu.Kan haka ne Garba Aliyu Zaria ya nemi ji daga bakin Barista Aliyu Zaria, lauya mai zaman kansa da ke birnin Legas, wanda ya yi tsokaci akan furucin na Gwamnan jihar ta Zamfara.

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari.
Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari. RFIHAUSA
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.