Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar Kastam ta kama kwantenonin Tramadol 35 a Najeriya

Daraktan hukumar tantance ingancin kayan abinci da magunguna na Najeriya NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, ta ce hukumar Kastam ta kama kwantenonin kwayar tramadol 35, a tashohi sauke kayayyaki daban daban da ke fadin kasar.

Tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke birnin Legas a tarayyar Najeriya.
Tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke birnin Legas a tarayyar Najeriya. REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Yayin zantawa da manema labarai a yau Lahadi, Farfesa Adeyeye ta ce tuni hukumar ta NAFDAC ta kone 9 daga cikin kwantenonin da aka mika mata, yayinda ta ke dakon mika mata sauran.

Sai dai shugabar hukumar ta NAFDAC, ta koka bisa tsaikon da ta ce suna fuskanta daga hukumar Kastam, wajen mika musu ragowar kwantenonin 26 da suka rage domin kone su.

Amfani da kwayar Tramadol a tsakanin matasa ba bisa ka’idar likita ba ta zama ruwan dare a Najeriya, duk da lalata kwakwal da ta ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.