Isa ga babban shafi
Najeriya

Jega ya soki 'yan majalisun Najeriya kan karbar cin hanci

Tsohon shugaban Hukumar Zaben Najeriya INEC, Farfesa Attahiru Jega ya soki mambobin Majalisar tarayyar kasar kan karbar cin hanci, in da ya ce shugabannin kwamitoci daban-daban a majalisar ne suka fi hatsari wajen karbar na goron.

Tsohon shugaban Hukumar Zaben Najeriya, Attahiru Jega
Tsohon shugaban Hukumar Zaben Najeriya, Attahiru Jega Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

Farfesa Jega ya bayyana haka ne a yayin gabatar da kasida mai taken “ gina zaman lafiya da kyakkyawan jagoranci don samun ci gaba mai dorewa a Najeriya” a birnin Abuja a jajibirin ranar demokradiya a kasar.

Jega wanda ya gabatar da kasidar a gaban dandzon mahalarta taron da suka hada da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da Alkalin Alkalan kasar, Walter Onnoghen ya ce, ‘yan majalisu na karbar cin hancin ne a karkashin fakewa da ayyukan kwamitocin.

Farfesan ya bayyana cewa, mambobun kwamitocin na yawaita rokon cin hanci don amincewa da kasafin kudin ma’aikatun gwamnati da na wasu hukumomi da zaran sun fita aikin sa ido.

Jega ya bukaci gwamnatin kasar da ta fadada yakin da ta ke yi kan cin hanci da rashawa  don ganin ya shafi hatta masu karbar na goro amma ba iya masu sace dukiyar kasa ba.

Sai dai tuni Majalisar Dattawan ta musanta kalaman Jega, in da ta kalubalance shi da ya wallafa sunayen sanatocin da suka bukaci karbar cin hanci, yayin da ta ce, matukar ya gaza bada sunayen, to lallai ya bai wa mambobinta hakuri.

Ba a karon farko kenan ba da ake zargin ‘yan majlisar da tilasta karbar irin wannan cin hancin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.