Isa ga babban shafi
Najeriya

Gobe Buhari ke cika shekaru 3 akan karagar mulki

Gobe ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke cika shekaru 3 a karagar mulki, kuma daga yau za mu rika kawo mu ku jerin rahotanni da hirarraki kan halin da ake ciki a bangarori daban daban kama daga kiwon lafiya, tattalin arziki, cin hanci da rashawa, tsaro da dai sauransu.

Lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu a shekarar 2015
Lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu a shekarar 2015 REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Za mu fara da bangaren kiwon lafiya wanda daya ne daga cikin muhimman bangarorin da gwamnatin Buhari ta yi alkawarin ingantawa tare daukan matakan rage yadda 'yan kasar ke tururuwa zuwa kasashen waje domin neman magani.

Yanzu haka ma’aikatan lafiyar kasar sun kwashe sama da makwanni 4 su na yajin aikin saboda abin da suka kira rashin kayan aiki da kuma daidata albashi.

Ko da dai shugaba Buharin ya nuna damuwa kan halin da yajin aikin zai jefa bangaren kiwon lafiya a fadin kasar.

Latsa alamar sauti da ke kasa don sauraron cikakkken rahoto game da halin da  bangaran kiwon lafiya a Najeriya ke ciki.

01:53

Rahoto kan kiwon lafiya a Najeriya

A lokacin da ya gana da wata tawagar likitoci a fadarsa da ke birnin Abuja a bara,  shugaba Buhari ya yi alkawarin kara zuba jari a bangaren kiwon lafiya da zimmar magance matsalar da ke tilasta wa kwararru a fannin kiwon lafiya ficewa daga kasar don zuwa aiki a wata kasa daban.

Sai dai har yanzu masana kiwon lafiya na ci gaba da bayyana bakin ciki kan yadda ake ci gaba da samun wannan matsalar ta ficewar likitoci daga Najeriya.

Gwamnatin Buhari ta dora laifin tabarbarewar bangaren lafiya kan gwamnatocin da suka gaba ce ta musamman gwamnatin da ya gada ta Goodluck Jonathan a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.