Shugabannin kabilar Igbo da ke Najeriya sun gudanar da wani taro, in da suka bukaci sake fasalin Najeriya da kuma biya musu wasu bukatu da suka gabatar domin ci gaba da dorewar kasar. Cikin bukatun nasu har da mayar da shugabanci sau daya na shekaru 6 ga shugaban kasa da gwamnoni da cire kananan hukumomi daga kundin tsarin mulki da kuma kirkiro musu karin Jiha. Dangane da wadanan bukatu nasu, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sanata Ibrahim Ida, tsohon Dan Majalisar Dattawa daga Jihar Katsina, wanda ya dade yana nazari da rubuce-rubuce kan sake fasalin Najeriya
Sauran kashi-kashi
-
Arewa maso Yammacin Najeriya ne mafi hatsari saboda matsalar tsaro - Bincike
Kungiyar 'Global Rights' ta bayyana yankin arewa maso yammacin Najeriya a matsayin mafi hadari, saboda yadda 'yan bindiga ke kisa da take hakkin Bil Adama ba tare da kaukautawa ba.18/04/202403:16 -
Kuskure ne a yi tunanin ɗagawar darajar naira ba zai ɗore ba - Dakta Kurfi
Darajar Naira na cigaba da ɗagawa a Najeriya tare da saukar farashin wasu kayayyakin abinci a wasu kasuwannin ƙasar, abinda ya sa wasu tunanin cewar tasirin saukar Dalar ne ya sanya wasu kayayyakin suka fara sauka.17/04/202403:19 -
Tattaunawa da Sanata Ikira Aliyu Bilbis kan tsaro a jihar Zamfara
Hukumomi a Najeriya daga matakin jiha zuwa na kasar baki ɗaya na daukar matakai daban daban wajen samar da zaman lafiya a jihar Zamfara, amma har ya zuwa wannan lokaci ba'a kai ga cimma biyan bukata ba.16/04/202403:26 -
Yadda rayuwa ta kasance bayan da muka faɗa hannun mayakan Boko Haram - Maryama
A ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilun nan aka cika shekaru 10 da sace dalibai mata na makarantar sakandaren Chibok sama da 250 da mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno.15/04/202403:17 -
Kwamred Bello Basi kan shirin gina hanyayoin zamani a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta sanar da kashe naira biliyan 4 kan kowacce kilomita ta hanyar zamani da ake ginawa daga jihar Legas zuwa birnin Kalaba.12/04/202403:40