Isa ga babban shafi
Najeriya

Amurka zata mayar wa Najeriya dala miliyan 500

Ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami yace shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai koma gida daga Amurka da albishir na maido da kudin kasar da aka sace, da ya kai dala miliyan 500.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ganawa da takwaransa na Amurka Donald Trump a Washington.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ganawa da takwaransa na Amurka Donald Trump a Washington. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Malami ya bayyana haka ne a hirar sa da manema labarai a birnin Washington, inda ya ce am cimma matasayar ce a tsakanin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Amurka Donald Trump, bayan ganawar da suka yi.

Najeriya ta dade tana kokarin karbo kudaden aka sace tare da boyesu a kasashen ketare, abinda ya zamar mata wani babban kalubale saboda sharudda da tarin , matakan da za a bi da kuma tsawon lokacin da kokarin ke shafewa kafin hakan ya tabbata.

A ranar 19 ga watan Janairu na shekarar 2016, Najeriya ta sa hannu yarjejeniyoyi 6 tsakaninta da Hadaddiyar Daular Larabawa, a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar, daga cikin yarjejeniyoyin akwai batun mikawa Najeriya kudaden da tsaffin mukarraban gwamnatin kasar suka sace, tare da boyewa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.