'Yan sandan Kano na farautar ceto Bajamushen da aka sace
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kaddamar da farautar ‘yan bindigan da suka sace wani Bajamushe a jiya Litinin bayan sun kashe dan sandan da ke tsaron sa.
Wallafawa ranar:
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Musa Majiya ya shaida wa RFI Hausa cewa, daga cikin matakan gaggawa da suke dauka don kubutar da Bajamushen, sun hada da baza jami’ansu akan hanyoyin shigowa da ficewa daga yankin da lamarin ya faru.
SP Majiya ya kuma tabbatar da mutuwar jami’in nasu da ‘yan bindigan suka hallaka har lahira.
Latsa nan don sauraren rahoto kan sace Bajamushe a Kano
Rahoto kan sace Bajamushe a Kano
Lamarin ya faru ne a unguwar Madobi da misanlin karfe 7:45 na safiya a dai dai lokacin da Bajamushen ya hallara don gudanar da wani aiki.
Baturen mai suna Michael Cremza, injiniya ne kuma yana aiki ne tare da kamfanin gine-gine na Dantata and Sawoe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu