Isa ga babban shafi
Najeriya

Ko menene gaskiyar ikirarin Salkida kan mutuwar 'yan Chibok?

Gwamnatin Najeriya ta ce, ba ta da masaniya game da mutuwar sauran 'yan matan Chibok kusan 100 da kungiyar Boko Haram ta sace kamar yadda Ahmed Salkida, dan jaridar da ke samun bayanai daga kungiyar ya yi ikirari a karshen mako. 

Wasu daga cikin 'yan matan Chibok da suka kubuta daga hannun Boko Haram
Wasu daga cikin 'yan matan Chibok da suka kubuta daga hannun Boko Haram REUTERS/Zanah Mustapha
Talla

Yayin da aka cika shekaru 4 da sace 'yan matan, Salkida wanda ke samun bayanai daga kungiyar Boko Haram kai tsaye, ya ce 'yan mata 15 suka saura da rai daga cikin 113 da ke hannun mayakan.

Dan jaridar ya ce, akasarin 'yan matan sun rasa rayukansu ne sakamakon hare-haren da sojoji ke kaddamar wa kan kungiyar kamar yadda majiyar Boko Haram ta shaida masa a cewarsa.

Salkida dai ya dauki tsawon lokaci yana bada cikakkun bayanai game da al’amurran da suka shafi kungiyar Boko Haram.

Wannan ne ya sa wasu daga cikin ‘yan Najeriya da suka hada da mambobin kungiyar fafutukar ceto ‘yan matan na Chibok Bring Back Our Girls ke ganin cewa, akwai kamshin gaskiya a bayanan Salkida.

Latsa nan don jin ra’ayoyin ‘yan Najeriya kan bayanin Salkida.

01:31

Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan bayanin Salkida game da mutuwar daliban Chibok

Wannan dai na zuwa ne a yayin da aka cika shekaru hudu da sace ‘yan matan Chibok 217, in da aka saki wasu ta hanyar tattaunawa, yayin da wasu suka samu nasarar tserewa.

A yayin mayar da martani, mai magana da yawun shugaban Najeriya, Garba Shehu ya ce, Salkida ba ya cikin tawagar gwamnatin kasar da ta jagoranci tattaunawar ceto ‘yan matan na Chibok sama da 100 daga hannun Boko Haram.

Shehu ya kara da cewa, kazalika dan jaridar ba ya cikin tawagar da a yanzu ke ci gaba da kokarin karbo sauran ‘yan matan.

Shugaba Buhari dai ya bukaci iyayen daliban na Chbok da su ci gaba da amanna game da kokarin gwamnatin kasar na ceto sauran ‘yan matan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.