Isa ga babban shafi
Najeriya

Kwastam ta kwace motoci 160 a gidan gwamnan Sokoto

Jami’an hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya watau Kwastam sun kai samame a gidan gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal tare da kwace motoci kusan 160 da hukumar ke zargin gwamnan da shigowa da su ba bisa ka’ida ba.

Gwamnan jihar Sokoto  Aminu Waziri Tambuwal da ake zargi da shigo da motoci kusan 160 ba bisa ka'ida ba don yakin neman zabensa a wa'adi na biyu
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da ake zargi da shigo da motoci kusan 160 ba bisa ka'ida ba don yakin neman zabensa a wa'adi na biyu dailypost
Talla

Wata majiya kwakkwara ta tabbatarwa sashen Hausa na RFI cewar, an gudanar da samamen ne jiya da dare, kuma wani lokaci a yau ne jami’an hukumar ta hana fasa kwauri, za su kira taron manema labarai dangane da wannan lamari.

Mutane da daman a ganin cewar gwamnan ya sayo Motocin ne da manufar yakin neman zabensa a wa’adi na biyu a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.