Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane na komawa Bama bayan Boko Haram ta kore su

Yanzu haka ana ci gaba da mayar da jama’a zuwa garin Bama da ke jihar Borno ta Najeriya, bayan share kusan shekaru 4 da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kwace garin tare da da fatattakar jama’a.

Mutane sun fara komawa garin Bama da ke jihar Borno bayan Boko Haram ta raba su da muhallansu
Mutane sun fara komawa garin Bama da ke jihar Borno bayan Boko Haram ta raba su da muhallansu REUTERS/Paul Carsten
Talla

Wakilinmu Bilyamin Yusuf da ya ziyarci yankin, ya ce gidaje sama da dubu 11 ne gwamnati ta gina a garin, a wani mataki na sassauta radadin da jama’a suka tsinci kansu a ciki sakamakon rikicin na Boko Haram.

Baba Kura Bulama na daya daga cikin wadanda suka koma gida, kuma a zantawarsa da RFI Hausa ya ce, gwamnati ta gyara mu su muhallansu tare da samar mu su da ruwan sha, baya ga tallafin abinci da ta ba su da suka hada da shinkafa da biski da garin masara da kuma mai da sinadarin magi.

Bulama ya bukaci sauran mazauna garin da ke ci gaba da zama a Maiduguri da su gaggauta komawa gida saboda a cewarsa, an ci galaban mayakan Boko Haram.

Kazalika gwamnatin ta gyara asibiti da makarantu da ke garin da ofisoshin ‘yan sanda, in da kuma ta girke jami’an tsaro don ci gaba da kare lafiyar jama’a.

Garin Bama dai shi ne na biyu mafi girma bayan Maiduguri, amma rikicin Boko Haram ya daidaita shi, kuma kimanin mako guda kenan da gwamnatin ta fara mayar da jama’a garin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.