Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta sake bayyana 'yan PDP da ta ce sun yi sata

Gwamnatin Najeriya ta sake bayyana sunayen mutanen da ta ce, sun sace dukiyar kasa a lokacin shugabancin Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP mai adawa.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana sunayen 'yan PDPn da ta ce sun wawure dukiyar kasar a lokacin jagorancin Goodluck Jonathan
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana sunayen 'yan PDPn da ta ce sun wawure dukiyar kasar a lokacin jagorancin Goodluck Jonathan REUTERS /Stringer
Talla

Ministan Yada Labaran Kasar Lai Muhammed ya bada sunayen mutane 23 a wata sanarwar da ya raba wa manema labarai da kuma kudin da ya ce sun sace.

Wasu daga cikin sunayen sun hada da Kanar Sambo Dasuki, tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da tsohuwar Ministar mai, Diezanni Allison Maduekwe da tsoffin hafsan sojin kasar, Janar Keneth Minimah da Janar Azubuike Ihejirika da Marshall Alex Bade.

Sauran sun hada da Inde Dikko, tsohon shugaban Kwastam da Sanata Bala Muhammed, tsohon ministan Abuja da tsoffin gwamnonin Niger da Plateau, Babangida Aliyu da Jonah Jang, da Nenadi Usman da Bashir Yuguda da Hassan Tukur.

Wannan dai na zuwa ne bayan jam'iyyar PDP mai adawa ta kalubalanci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta bayyana sunayen 'yan PDPn da suka wawure dukiyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.