Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kashe mutane 18 a jihar Borno

Mayakan Boko Haram sun kaddamar da farmaki kan sansanin sojin Najeriya da kuma wasu kauyuka biyu da ke kusa da birnin Maiduguri da ke jihar Borno, in da suka kashe mutane akalla 18 tare da jikkata 84.

Ana ganin mayakan sun shirya tsaf kafin kaddamar da farmakin a cikin daren jiya
Ana ganin mayakan sun shirya tsaf kafin kaddamar da farmakin a cikin daren jiya © AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Harin dai na daya daga cikin munanan hare-haren da aka kaddamar a 'yan watannin baya-bayan nan, kuma ana ganin sai da suka yi kyakkyawan shiri kafin kai farmakin.

Mayakan sun yi amfani da bama-bamai da igwa da kuma bindigogi wajen kaddamar da harin wanda ya kai ga musayar wuta tsakaninsu da jami'an tsaro kamar yadda wani babban jami’in sojin kasar ya tabbatar.

Jami’in wanda ya bukaci a sakaya sunasa ya ce, mayakn sun iso ne a kafa kuma mutun bakwai daga cikinsu ne suka kai harin kunar bakin wake a kauyukan Bale Shuwar da Alikaranti.

Mayakan sun kashe mutane ne a yayin da suke kokarin tserewa daga kauyan kamar yadda majiyar tsaro ta tabbatar.

Wakilinmu da ke birnin Maiduguri, Bilyaminu Yusuf ya tabbatar mana da jin karar bama-bamai a yayin kai farmakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.