Isa ga babban shafi
Najeriya

Bai kamata 'yan Najeriya su amince da PDP ba - Tinubu

Daya daga cikin dattawan jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Bola Tinubu, ya shawarci ‘yan Najeriya, da cewa kada su amince da neman afuwar da jam’iyyar adawa ta PDP ta yi dangane da kura kuran da ta tafka a lokacin da ta jagoranci kasar tsawon shekaru 16.

Daya daga cikin dattawan Jam'iyya mai mulki ta APC a Najeriya, Bola Tinubu.
Daya daga cikin dattawan Jam'iyya mai mulki ta APC a Najeriya, Bola Tinubu. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Tinubu ya bayyana haka ne yayin da ya ke gabatar jawabi a birnin Legas, inda aka gabatar da bikin taya shi murnar cika shekaru 66.

Tsohon gwamnan jihar ta Legas, ya bayyana hakurin da da shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus ya bai wa ‘yan Najeriya a matsayin Yaudara ga ‘yan kasar don cimma manufar siyasa.

A cewar Tinubu, afuwar da jam’iyyar adawar ta nema ba zai gyara barnar da tafkawa ‘yan Najeriya ba tsawon shekaru 16, wadda ake ganin sakamakonta a yanzu.

Yayin gabatar da nashi jawabin, mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce, dala biliyan 3 suka bata sakamakon wata yarjejeniyar kasuwancin da kamfanin NNPC ya kulla tsakanin sa da wasu Yan kasuwa a karkashin gwamnatin da ta shude ta PDP.

Farfesa Osinbajo ya ce gwamnatinsu ta yi nasarar sanya naira biliyan 500 a shirin tallafawa masu karamin karfi, rage radadin talauci da samar da ayyukan yi, shirin da ya ce shi ne irinsa mafi girma a tarihin Najeriya da kuma nahiyar Afrika yankin kudu da Sahara.

Mataimakin shugaban Najeriyar, ya kara da cewa gwamnatin yanzu ta cinmma wannan nasarar ce, duk da cewa bayan kafuwarta a shekarar 2015, farashin gangar danyen mai a kasuwar duniya ta fadi da sama da kashi 50%, kuma a dai shekarar yawan gangar danyen man da Najeriya ke hakowa ya ragu daga miliyan 2 zuwa kasa da miliyan guda, saboda hare haren tsagerun yankin Niger Delta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.