Isa ga babban shafi
Najeriya

Za mu yi sahihin Zabe a 2019- Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa Majalisar Dinkin Duniya cewa, Najeriya za ta gudanar da sahihin zaben shugaban kasa a shekarar 2019.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS /Stringer
Talla

Shugaba Buhari ya bada tabbacin ne a yayin ganawarsa da Mataimakiyar Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Amina Muhammed a birnin tarayya Abuja.

Buhari ya yi marhabin da goyon bayan Majalisar a yayin da kasar ke ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben a badi.

Amina Mohammed ta zanta da Buhari akan abubuwa da dama da suka shafi zabe da tasa keyar ‘yan gudun hijirar Kamaru da kasuwancin bai daya a nahiyar Afrika da kuma matsalar tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.