Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun hallaka masunta 5

Mayakan Boko Haram sun hallaka wasu masunta 5 sakamakon gudunmawar da suke bai wa jami’an tsaron Najeriya wajen neman inda mayakan suka boye, daliban makarantar ‘yan mata ta Dapchi.

Wasu masunta a Tafkin Chadi.
Wasu masunta a Tafkin Chadi. AFP Photo/PHILIPPE DESMAZES
Talla

Shugaban kungiyar masunta na jihar Borno, Abubakar Gamandi, ya ce harin na Boko Haram ya auku ne Tudun Umbrell wani tsibiri da ke tankin tafkin Chadi, wanda yayi iyaka tsakanin najeriya da kasashen Kamaru da Chadi.

Shugaban kungiyar masunta ya bada tabbacin cewa ‘ya’yan kungiyar tasa da mayakan na Boko Haram suka hallaka suna taimakawa sojin Najeriya wajen neman inda aka boye daliban saboda sun san duk wani lungu da sako na yankin.

A wani labarin kuma gwamnatin Najeriya, ta jadadda kwarin gwiwar kubutar da daliban na makarantar Dapchi, kasancewar sojin kasar suna ci gaba da kusantar samun nasarar cimma mayakan Boko Haram da suka sace su.

Ministan tsaron Najeriya Masur Dan-Ali ne ya bada tabbacin, yayin wata tattaunawa da ya yi, da wata kafar talabijin a Abuja.

A baya bayan nan ne shugaban najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa hukumomin tsaron kasar umarnin su tabbatar da ceto dukkanin ‘yan kasar da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su, ciki har da ragowar daliban makarantar Chibok da aka sace su a shekarar 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.