Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Filato ta kafa dokar hana zirga-zirga

Gwamnatin Jihar Filato da ke Najeriya ta sanar da kafa dokar hana zirga-zirga daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safe a karamar hukumar Bassa dake fama da tashin hankali.

Hadikwatar rundunar musamman ta samar da tsaro a jihar Filato ta "Operation Safe Haven"
Hadikwatar rundunar musamman ta samar da tsaro a jihar Filato ta "Operation Safe Haven" nta.ng
Talla

Sakataren Gwamnatin Jihar Rufus Bature ya sanya hannu kan sanarwar, bayan wasu jerin hare haren da aka samu wadanda suka kai ga rasa rayuka.

A baya bayan nan wani kazamin rikici da aka tafka tsakanin matasan Irigwe da na Fulani a yankin Miango da ke karamar hukumar Bassa, ya yi sanadin hallaka jami’an tsaro 2 da ke karkashin rundunar samar da tsaro a jihar Filato ta "Operation Safe Haven".

Kakakin rundunar sojin ta musamman Manjo Adam Umar wanda ya tabbatar da hallaka jami’an nasu, ya ce an kuma kone gidaje da dama sakamakon rikicin da ya faru a safiyar ranar Laraba, inda ya ce ba’a kammala kidaya hasarar rayukan da aka samu ba.

Sai dai Manjo Umar ya ce sun samu nasarar kama mutane takwas daga bangarorin biyu masu rikici da juna, dukkaninsu dauke da muggan makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.