Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Abdullahi Tata kan ziyarar Buhari a Benue

Wallafawa ranar:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda a jiya Litinin ya ziyarci jihar Benue da ke fama da rikici tsakanin manoma da makiyaya, ya ce ya damu matuka dangane da yawaitar hare-hare da kan yi sanadiyyar mutuwar mutane da asarar dukiya mai tarin yawa a jihar.To sai dai wani abu da ya fi daukar hankulan jama’a shi ne yadda shugaban ya ce ya yi mamaki dangane da yadda sufeton ‘yan sandar kasar Ibrahim Idris ya ki karbar umurnin da ya ba shi na ya tare a jihar ta Benue har zuwa lokacin da hankula suka kwanta. Akan haka ne AbdulKarim Ibrahim Shikal ya tattauna da Alhaji Umar Abdullahi Tata, masani harkokin mulki, sannan kuma dan siyasa daga jam’iyyar adawa ta PDP.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Shannon Stapleton
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.