Mèdecins Sans Frontières ta janye jami'anta daga Rann
Kungiyar likitocin kasa da kasa, ta Mèdecins sans Frontières ta ce ta dakatar da ayyukan jami’anta a garin Rann da ke jihar Borno, tare da kwashe su, biyo bayan farmakin da mayakan Boko Haram suka kai inda suka hallaka musu jami’ai 3.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Matakin yana kunshe cikin sanawar da kungiyar likitocin ta Mèdecins sans Frontières ta fitar, inda ta yi Karin bayanin cewa ta janye ma’aikatanta na cikin Najeriya da na waje guda 22.
A ranar Alhamis da ta gabata, mayakan na Boko Haram suka kai wa wani barikin sojojin Najeriya hari a garin na Rann, inda suka hallaka akalla mutane 11, ciki har da ma’aikatan lafiyar na Mèdecins sans Frontières 3.
Har yanzu dai babu tabbacin iyaka yawan wadanda suka hallaka da kuma wadanda harin ya jikkata. Sai dai jami’an agajin na Mèdecins sans Frontières, sun ce sun bai wa akalla mutane 9 kulawa sakamakon jikkatar da suka yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu