Isa ga babban shafi
Najeriya

Daliban makarantar Dapchi suna hannun mu - Al-Barnawi

Tsagin kungiyar Boko Haram da ke karkashin shugabancin Abu Musab al Barnawi ya yi ikirarin mayakansa ne suka sace daliban makarantar sakandaren ‘yan mata ta Dapchi.

Jagoran tsagin kungiyar Boko Haram da ya yi ikirarin daliban Dapchi suna hannunsu, Abu Musab Al-Barnawi, dan tsohon shugaban kungiyar Muhammad Yusuf.
Jagoran tsagin kungiyar Boko Haram da ya yi ikirarin daliban Dapchi suna hannunsu, Abu Musab Al-Barnawi, dan tsohon shugaban kungiyar Muhammad Yusuf. Guardian Nigeria
Talla

Mai rajin kare hakkin dan adam a Najeriya Aisha Wakil da ta taba zama manba a kwamitin tattaunawa da mayakan a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan, ta bayyana cewa mayakan sun tuntube ta dangane da daliban, a wata ganawa da ta yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN.

Aisha Wakil ta ce mayakan sun shaida mata cewa, daliban suna cikin yanayi mai kyau da kuma koshin lafiya, zalika a shirye suke su sako ‘yan matan daga garkuwar da suka yi da su.

Sai dai bata bayyana iyaka yawan daliban da ke hannun mayakan ba, wadanda aka ce an sace 110.

Al- Barnawi dan fari ne ga shugaban kungiyar Boko Haram Muhammad Yusuf, wanda ya kafa ta.

A watan Agustan shekarar 2016, kungiyar ISIS ta zabi Al-Barnawi, a matsayin shugaban kungiyar Boko Haram, matakin da Abubakar Shekau jagoran kungiyar na baya, ya ce ba zai taba amincewa da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.