Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sandan Najeriya na bincike kan rikicin Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna da ke Najeriya ta kaddamar da bincike kan musabbabin rikici tsakanin ‘yan Kabilar Kadara da Hausawa a kasuwar Magani da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7 tare da jikkatar 15.

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Naseer El Rufa'i ya bada umarnin gurfanar da masu hannu a rikicin Kasuwar Magani
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Naseer El Rufa'i ya bada umarnin gurfanar da masu hannu a rikicin Kasuwar Magani Premium Times
Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Mukhtar Hussain ne ya bayyana haka a hirarsa da RFI Hausa, in da ya ce tuni suka cafke mutane 10 da ake zargi da hannu a hatsaniyar wadda ta barke a karamar hukumar Kajuru.

Rikicin ya kuma harzuka wasu matasa da suka fantsama cikin gari tare da cinnawa gidaje da shaguna da otel wuta.

Wasu shaidu sun alakanta tashin hankalin da wata mata da ta bayyana aniyarta ta sauya addini, lamarin da ya sa bangarorin mabiya addinan biyu suka fara hatsaniyar da ta rikide ta koma mummunan rikici har ta kai ga soke-soken wukake.

Gwamnan jihar ta Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya bada umarnin gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a tashin hankalin.

Jihar Kaduna ta yi kaurin suna wajen rikicin kabilanci da addini musamman a shekarun baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.