Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 20/08 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 20/08 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 20/08 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 20/08 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/08 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/08 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 20/08 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 20/08 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 20/08 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Najeriya

Boko Haram ta yi safarar 'yan matan Dapchi zuwa Nijar

media Wasu daga cikin 'yan matan makarantar Dapchi da suka ce sun tsira a yayin farmakin Boko Haram da ta sace dalibai sama da 100 a makarantarsu ta Sakandare a Yobe REUTERS/Ola Lanre

An yi safarar rabin ‘yan matan makarantar Dapchi da kungiyar Boko Haram ta sace a makon jiya a jihar Yobe ta Najeriya zuwa Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da kasar.

Wasu majiyoyi sun shaida wa jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar cewa, kungiyar Boko Haram ta raba matan gida biyu, in da ta ajiye kashi daya a garin Tumbum Gini da ke karamar hukumar Abadam a jihar Borno a Najeriya, yayin da ta yi amfani da jirgin ruwa wajen safarar kashi na biyu zuwa wani kauye da ke garin Duro a Nijar.

Rahotanni na cewa, tsagin mayakan Boko Haram karkashin jagorancin Musab Albarnawi ne ya sace ‘yan matan da yawansu ya kai 110 a ranar Litinin da ta gabata a Yobe kamar yadda mahukuntan kasar suka tabbatar da adadinsu.

Gwamnan jihar yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam ya dora laifin sace daliban akan janyewar dakarun sojin kasar daga yankin, amma rundunar sojin ta musanta haka.

Gwamnan jihar Borno da ya kai wa Gaidam ziyarar jaje, Kashim Shettima ya ce, sace daliban ya tuna ma sa da sace ‘yan matan makarantar Chibok a shekarar 2014.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure