Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun ceto 70 daga cikin daliban makarantar Dapchi

Rundunar Sojin Najeriya ta samu nasarar ceto dalibai sama da 70 da suka bata sakamakon harin da kungiyar Boko Haram ta kai makarantar ‘Yan mata dake Dapci a Jihar Yobe.

Wasu jami'an sojin Najeriya.
Wasu jami'an sojin Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Rahotanni daga garin na Dapci da kuma majiyar jami’an tsaro, sun tabbatar da kubutar da ‘Yan matan, kuma yau ake sa ran mika su ga jami’an gwamnati domin tantance lafiyar su, da kuma mika su ga iyayen su.

Bayanai sun ce, biyu daga cikin ‘Yan matan sun rasa rayukan su, lokacin kubutar da su.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci ministoci 3 a karkashin jagorancin Ministan tsaro Janar Masur Dan Ali su tafi jihar ta Yobe.

Yayin zantawa da Sashin Hausa na RFI, Janar Mansur Dan Ali ya bukaci dukkanin jama’a da su rika bada gudunmawa wajen samar da tsaro ba zurawa jami’an tsaro kadai idanu ba.

01:09

Muryar Ministan tsaron Najeriya Janar Mansur Dan Ali

Kabir Yusuf

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.