Isa ga babban shafi
Najeriya

Ci Gaba Da Kisan Jama'a A Zamfara Na Tada Hankalin Gwamnatin Najeriya

Bisa dukkan alamu ci gaba da kisan bayin Allah a jihar Zamfara na Nigeria ya tasar da hankulan mahukuntan Najeriya  da tilasta masu maida hankula jihar a yanzu haka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari rfi
Talla

Ministan Tsaro Mansur Dan Ali wanda dan asalin jihar ce ya koma jihar domin ganin an dauki matakan magance lamarin.

Shima Babban Sufeto Janar na 'Yan Sandan kasar Ibrahim Idris na jihar Zamfara tare da ayarin manyan 'yan sanda domin tattauna irin matakan da suka dace a dauka.

Ibrahim Idris har ya ziyarci Sarkin  Zurmi Alhaji Abubakar Atiku Mohammed inda yake  cewa yawan kisa da ake samu a Zamfara na neman wuce gona da iri.

Tsakiyar makon daya gabata ne wasu 'yan bindiga suka kashe mutane 40 a kauyen Birane dake karamar hukumar Zurmi.

Wannan shine na baya-bayan nan kisa da ake samu akai-akai a jihar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.