Isa ga babban shafi
Najeriya

Tsohon Shugaba Jonathan Ya Goyi Bayan Zaben Shugaban Kasa A Karshen Duk Zabuka

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya goyi bayan majalisar Kasar na sauya tsarin zabukan kasar da za’a yi a shekara ta 2019 domin zaben shugaban kasa yazo na karshe a jerin zabukan.

Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan yayinda yake mikawa Muhammadu Buhari ragamar mulki
Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan yayinda yake mikawa Muhammadu Buhari ragamar mulki rfi
Talla

Wata sanarwa da sa hannun Ike Abonyi mashawarcin tsohon shugaban kasar na cewa matakin da majalisar Najeriya ta dauka zai taimaka don ganin ana zaben dan takara bisa chanchanta ne ba sai mutun ya dogara da wani ba.

Talata da ta gabata ne dai Komitin zabe na Majalisar kasar Nigeria ya gabatar da shirin doka dake nuna zaben shugaban kasa zai zo na karshe a jerin zabukan da za’a yi a shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.