Isa ga babban shafi
Najeriya

An samu baraka a majalisar dattawan Najeriya kan zaben 2019

Baraka ta kunno kai a tsakanin ‘yan Majalisar Dattawan Najeriya kan amincewa da sabuwar dokar zabe wadda ta fayyace cewar zaben shugaban kasa shi zai zama na karshe a shekara mai zuwa.

Zauren majalisar dattawan Najeriya.
Zauren majalisar dattawan Najeriya. National Assembly
Talla

Zauren Majalisun Dattawa da na Wakilan Najeriya ne suka fara amincewa da sauya tsarin manyan zabukan kasar, inda aka saba gabatar da zaben shugaban kasa, na ‘yan majalisun tarayya, sai kuma na gwamnoni daga karshe, kamar yadda hukumar shirya zaben kasar INEC ta tsara yi a 2019.

Karkashin sabon tsarin na yanzu, za’a fara ne da zaben ‘yan majalisun tarayya, Gwamnoni, sannan na shugaban kasa ya biyo baya.

Wasu ‘yan majalisun da suka haure takalman su suka fice daga majalisar a karkashin Sanata Abdullahi Adamu, sun gana da manema labarai inda suka bayyana rashin amincewar su da yadda aka amince da dokar.

‘Yan majalisun da suke adawa da sauyin yi zargin cewa, akwai makarkashiyar da aka shirya domin haddasa matsala ga kokarin sake zabar shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Sai dai wadanda ke goyon bayan sauyin sun ikirarin cewa, wannan ba shi ne karo na farko da aka samu sauyin faraway da zaben ‘yan majalisu ba.

Yayin zantawar sa da Sashin Hausa na RFI, Sanata Ali Wakili daga Jihar Bauchi daya daga cikin wadanda basa goyon bayan sauyin ya ce, bayan ra’ayin al’ummar da yake wakilta na kin amincewa da sauyin, sabon tsarin gudanar da zaben, yana tattare da kashe kudade fiye da na baya.

00:37

Sanata Ali Wakili: An samu baraka a majalisar dattawan Najeriya kan zaben 2019

Bashir Ibrahim Idris

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.