Bakonmu a Yau
Sakataren Gwamnatin Najeriya Boss Mustapha kan tsaikon rantsar da shugabannin gudanar da hukumomin gwamnati
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:21
‘Yan Najeriya sun fara bayyana korafin su kan yadda sama da wata guda bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada shugabannin gudanar hukumomin gwamnati, kuma har yanzu ba'a rantsar da su ba, domin gudanar da aikin dake gaban su. Rashin wadannan shugabanin dai na yi wa aikin hukumomin tarnaki. A kan haka ne wakilinmu a Abuja, Muhammad Kabir Yusuf, ya tattauna da Sakataren Gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha.