Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun kubutar da mutane 84 daga hannun Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana samun nasarar ceto mutane 84 da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da su tsawon shekaru 3, a sansanin kungiyar na Camp Zero da ke dajin Sambisa.

Sojin Najeriya yayin da suke shiga garin Damboa a jihiar Borno 25 ga watan Maris, 2016.
Sojin Najeriya yayin da suke shiga garin Damboa a jihiar Borno 25 ga watan Maris, 2016. STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

Ya yin zantawa da manema labarai a garin Maiduguri Kwamandan rundunar sojin Najeriyar ta musamman, mai taken “Operation Lafiya Dole”, Manjo Janar Rogers Nicholas, ya ce, sun mika mutanen zuwa ga hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno SEMA.

Kwamndan ya ce wasu daga cikin matan da aka ceto suna dauke da juna biyu, yayin da yunwa ta kama mafi akasarin kananan yaran dake ciki.

A wani labarin kuma, Manjo Janar Rogers Nicholas, ya ce Rabi Abu-Yasir, mai dakin likitan jagoran mayakan Boko Haram Abubakar Shekau ta mika kanta ga jami'an tsaron Najeriyar.

Rabi ta bayyana cewa maigidan nata yana kuma lura da ayyukan yi wa mayakan kungiyar ta Boko Haram tiyata.

A ranar Talata da ta gabata, rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun sake samun nasarori kan farmakin da suke ci gaba da kai wa kungiyar Boko Haram a Sambisa, domin karasa kakkabe ragowar mayakan kungiyar daga dajin.

Daraktan hulda da Jama’a na rundunar Brigediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ya bayyana haka, cikin sanawar da ya fitar a garin Maiduguri a waccan lokacin.

KukaSheka ya ce dakarun Najeriya tare da taimakon jiragen yaki, sun hallaka mayakan Boko Haram 7, tare da lalata motocin yaki masu dauke da manyan bindigogi 11, da kuma wasu motocin 12, a sansanin ‘camp zero’, yayinda suka kwace wata motar yakin makare da makamai daga hannun mayakan.

Mayakan kungiyar ta Boko Haram da dama ne suka tsere dauke da raunuka, dalilin da ya sa rundunar sojin Najeriyar ta bukaci taimakon al'ummar da ke zaune a yankunan arewa maso gabashin kasar, wajen bada rahoton gano maboyar mayakan idan suka yi katarin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.