Najeriya:IPMAN ta kammala shirin fara aikin gina sabbin matatun mai
Kungiyar dillalan man fertur ta Najeriya IPMAN ta ce ta kammala shirin fara aikin gina sabbin matatun mai a jihohi biyu na kasar akan kudi dala biliyan 3, kwatankwacin naira Triliyan 1.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban kungiyar IPMAN ta kasa, Mista Chinedu Okoronkwo ne ya bayyana haka, yayin zantawar da ya yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN a birnin Legas.
A watan Yulin shekarar 2014, IPMAN ta sayi fili mai fadin Kadada dubu daya, domin gina matatun man a Itobe da ke jihar Kogi, da kuma Abbe a jihar Bayelsa.
Ana sa ran bayan kammala matatun, za su rika tace gan-gar tataccen man fetur dubu 200,000 a kowacce rana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu