Isa ga babban shafi

"Sojojin Najeriya suna ci gaba da samun nasara a Sambisa"

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun sake samun nasarori kan farmakin da suke ci gaba da kai wa kungiyar Boko Haram a Sambisa, domin karasa kakkabe ragowar mayakan kungiyar daga dajin.

Wasu jami'an sojin Najeriya.
Wasu jami'an sojin Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Daraktan hulda da Jama’a na rundunar Brigediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ya bayyana haka, cikin sanawar da ya fitar a garin Maiduguri.

KukaSheka ya ce dakarun Najeriya tare da taimakon jiragen yaki, sun hallaka mayakan Boko Haram 7, tare da lalata motocin yaki masu dauke da manyan bindigogi 11, da kuma wasu motocin 12, a sansanin ‘camp zero’, yayinda suka kwace wata motar yakin makare da makamai daga hannun mayakan.

Mayakan kungiyar ta Boko Haram da dama ne suka tsere dauke da raunuka, dalilin da ya sa rundunar sojin Najeriyar ta bukaci taimakon al'ummar da ke zaune a yankunan arewa maso gabashin kasar, wajen bada rahoton gano maboyar mayakan idan suka yi katarin haka.

Kakakin sojin Najeriyar, ya ce jami’ai biyu ne kawai suka jikkata, wadanda a yanzu ke karbar magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.