Gwamnatin Borno ta sassauta dokar hana zirga-zirga
Gwamnatin Jihar Borno ta sassauta dokar hana zirga-zirgar da ta kafa a birnin Maiduguri da awanni biyu.
Wallafawa ranar:
Kwamishinan yada Labaran Jihar Dr Muhd Bulama, ya ce a yanzu dokar hana zirga-zirgar zata fara aiki ne daga karfe 10:30 na dare, zuwa karfe 6:00 na safe.
To sai dai gwamnatin jihar ta ce yankunan Moloi da Muna Garage zasu ci gaba da kasancewa a karkashin dokar hana zirga-zirgar daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe.
Kafin sassaucin, makwanni uku birnin Maiduguri ya shafe a karkashin dokar hana zirga-zirgar da ke farawa daga karfe 8:00 na dare, zuwa karfe 6:00 na safe.
A waccan lokacin karo na uku kenan da gwamnatin Jihar ta Borno ta kara wa’adin, bisa shawarar rundunar sojin Najeriya, domin bai wa rundunar karin lokaci na daukar matakan tabbatar da cikakken tsaro a birnin na Maiduguri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu