Bakonmu a Yau
Kakakin ‘yan sandan jihar Kaduna ASP Mukhtar Aliyu kan sace turawa 2 a Kaduna
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:23
Duk da matakan tsaro da ake ke dauka don yakar yawaitar sace mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, wasu gun-gun mutane da ake kyautata zaton cewa, masu sata da kuma garkuwa da mutane ne, sun hallaka wasu ‘yan sanda 2, tare da sace turawa 2 da jami’an ke bai wa tsaro. Turawan suna kan hanyar dawowa ne daga ziyartar kananan hukumomin Kafanchan da Kaura inda gun-gun mutanen suka yi musu kwanton Bauna. Garba Aliyu Zaria ya tattauna da kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ASP Mukhtar Aliyu, wanda ya yi Karin haske kan halin da ake ciki.