Isa ga babban shafi
Najeriya

Na gargadi Ortom kan zartas da dokar hana kiwo a Benue - Lalong

Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong, ya ce ya gargadi takwaransa, gwamnan Benue Samuel Ortom, akan ya kaucewa kafa dokar haramtawa makiyaya kiwo a Jihar.

Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong.
Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong. Nigerian Monitor
Talla

Gwamna Lalong ya bayyana haka ne a garin Abuja, bayan ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a kan matsalar rikicin manoma da makiyaya da ke dada girmama a sassan kasar, musamman kashe kashen da aka samu a baya bayan-nan a jihar Benue.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai, Lalong ya ce a fahimtarsa, hanya mafi gaggawa da gwamnati zata bi wajen kawo karshen wannan babbar matsala, ita ce, samar da isassun filayen da zasu bai wa makiyaya damar gudanar da kiwo na zamani, tare da samar da hanyoyi da dabbobi zasu rika bi.

Gwamnan Jihar Filaton ya ce a lokacin da takwaransa na Benue, Samuel Ortom ke nazari zartas da dokar haramta kiwo a jihar, ya gargade shi da cewa daukar matakin ba shi ne mafita ba, sai dai ma ya haifar da wata sabuwar matsalar, wadda kuma za’a iya alakanta ta da kashe-kashen da aka samu na bada dadewa ba.

A halin da ake ciki, tuni Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya koma jihar Benue da zama, bisa umarnin shugaban kasa, domin tabbatar da cewa an magance kashe-kashen da ake samu.

Sai dai lokacin da yake mayar da martani kan muhawarar da dokar da ya kafa ta haramta kiwo ta haifar, gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom, ya ce kafa dokar ya zama dole, domin ita ce hanya mafi dacewa ta magance rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar.

Wakilinmu daga Abuja Kabiru Yusuf ya ji ta bakin bangarorin guda biyu, kamar yadda za'a saurara cikin rahotonsa.

01:30

Na gargadi Ortom kan zartas da dokar hana kiwo - Lalong

Kabir Yusuf

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.