Super Eagles za ta fafata da Ingila
To mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya super Eagles Gernot Rohr ya tabbatar da cewa ‘yan wasan Najeriyar za su fafata da takwarorinsu na Birtaniya a wasannin sada zumunta gabanin wasan cin kofin duniya da zai gudana a Rasha.
Wallafawa ranar:
Rohr yayin tattaunawarsa da manema labarai ya ce Super Eagles za ta kece raini da ‘yan wasan na Ingila ranar 2 ga watan Yuli a filin wasa na Wembley da ke birnin London.
Kasashen biyu na Ingila da Najeriya na cikin rukuni na uku a wasannin cin kofin duniya da zai gudana.
Kocin Najeriyar ya ce fafatawar abar alfahari ce kuma dama ce ta yadda ‘yan wasan na Super Eagles za su nuna bajintarsu ga zakarun duniya na 1966.
Tuni dai mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa na farko a Najeriya Seyi Akinwunmi ya ce matakin wasan babban ci gaba ne ga Super Eagles.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu