Isa ga babban shafi
Najeriya

Mun murkushe mayakan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi - Buratai

Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi shelar samun nasarar murkushe mayakan kungiyar Boko Haram a yankin tafkin Chadi da kuma arewacin jihar Borno.

Babban Hafsan Sojin Najeriya Lafatanar Janar Yusuf Tukur Buratai.
Babban Hafsan Sojin Najeriya Lafatanar Janar Yusuf Tukur Buratai. AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Buratai ya ce, a halin yanzu sojojin Najeriya sun mayar da hankali ne kan tabbatar da tsaron da suka samar a yankunan da suka kwace daga hannun mayakan.

Babban hafsan sojin Najeriyar, ya bayyana haka ne, a lokacin da ya kai wa bataliya ta 8 ziyara a garin Munguno, inda ya ce ana gaf da karasa kawar da dukkanin barazanar mayakan na Boko Haram, duk da hare-haren da suka hada dana kunar bakin wake, da suke ci gaba da kai wa a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.

Lafatanar Kanal Buratai ya kuma yabawa rundunar sojin saman Najeriya dangane da irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.