Isa ga babban shafi
Kaduna

Kaduna: 'Yan bindiga sun hallaka Sarkin Gwantu

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe Sarkin Gwantu wato Etum Numana a karamar hukumar Sanga, da ke jihar Kaduna a tarayyar Najeriya.

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Naseer El Rufa'i.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Naseer El Rufa'i. Premium Times
Talla

‘Yan bindigar sun kuma hallaka matar Sarkin, yayin da suka yi wa dansa rauni ta hanyar harbi da bindiga.

Lamarin ya faru ne a cikin daren jiya Lahadi, kuma wakilinmu Aminu Manu, ya ziyarci asibiti inda ake jinyar daya dada cikin ‘ya’yan sarkin da ya samu rauni wato Dan Azumi Makama, wanda ya yi masa karin bayani dangane da yadda lamarin ya faru.

00:54

Najeriya-Kaduna-Dan Azumi Makama-2018-01-01

Abdoulkarim Ibrahim

Gwmnatin Kaduna ta tabbatar da faruwar wannan lamari, kuma a cewar kakakinta Samuel Aruwan, tuni aka bai wa jami’an tsaro umarnin fara bincike don gano wadanda ke da hannu a kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.