Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya jajantawa ‘yan Najeriya kan matsalar man fetir

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tausaya ‘Yan Najeriya kan halin kuncin da suka samu kan su sakamakon karancin man fetir da ya jefa al’ummar kasar cikin kuncin rayuwa.

Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A wasikar da ya rubutawa al’ummar kasar, shugaban ya ce yana bin halin da ake ciki sau da kafa, kuma yana samun bayanai daga kamfanin man NNPC kan kokarin da ake wajen shawo kan matsalar, inda ya ke cewa nan bada dadewa ba man zai wadata.

Jam’iyyar PDP mai adawa ta zargi shugaban da gazawa wajen karancin man musamman a wannan lokaci na bukukuwan kirsimeti da karhen shekara.

Shugaban kungiyar dattawan Igbo na Ohaneze John Nwodo ya ce da gan-gan gwamnati ta haifar da matsalar domin kuntatawa 'yan kabilar su.

Tsohon Ministan ilimi a Najeriya Oby Ezekwesili ta shawarci shugaba Buhari ya ajiye mukaminsa na Ministan Man kasar, inda ta ke cewa haka ne ka wai zai rage siyasar da fannin ke fuskanta.

Tun tsanantar wahalar Man 'yan Najeriya ke siyan litar guda na Fetir akan naira 400 zuwa 600 a wasu yankunan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.