Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Za'a fara yi wa jami'an 'yan sanda gwajin kwakwalwa

Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris, ya ce za’a fara aiwatar da shirin yin gwajin lafiyar kwakwalwa ga jami’an ‘yan sandan kasar na runduna ta musamman mai yaki da fashi da makami da sauran manyan laifuka da aka fi sani da SARS.

Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris.
Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris. independent.ng
Talla

Sifeto janar din ya bayyana shirin fara aiwatar da matakin ne a garin Abuja, yayin ganawa da kwamandojin rundunar ta SARS daga sassan Najeriya.

Ya ce matakin yana a matsayin yi wa rundunar ta SARS garambawul domin tabbatar da kwarewar jami’an sashin rundunar, da kuma kawo karshen yawaitar samun hallaka fararen hula da jami’an rundunar ke yi ba bisa hakki ba.

Sifeto janar Ibrahim Idris, ya kuma yi gargadi jami’an na SARS da su kaucewa shiga al’amuran da bai safe su ba, zalika za’a dauki tsattsauran mataki kan duk jami’an ya sabawa wannan umarni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.