Isa ga babban shafi
Najeriya

"Wasu daga cikin jami'an agaji basa neman taimakon jami'an tsaro"

Rundunar bayar da tsaro ta Civil Defence a Maiduguri ta ce wasu daga cikin jami’an bayar da agaji da ke aiki a jihar ko sauran yankuna masu fama da matsalar tsaro, basa neman rakiyar jami’an tsaro kamar yadda ya kamata.

Jagoran mayakan Boko Haram Abubakar Shekau.
Jagoran mayakan Boko Haram Abubakar Shekau. © AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, Alhaji Abdullahi Ibrahim kwamandan rundunar ta Civil Defence da ke Maiduguri, ya ce mafi akasarin jami’an agajin suna aikata kuskuren ne, bisa tunanin karfin mayakan ya lafa, sakamakon galabar da sojojin Najeriya ke samu kan ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

A ranar Asabar da ta gabata ne wasu mayakan kungiyar Boko Haram suka kai wa tawagar motocin jami’an agaji na majalisar dinkin duniya farmaki a jihar Bornon Najeriya tare da hallaka mutune 4 baya ga kwashe tarin kayayyakin abinci.

Yawaitar kai hare-hare kan Jami’an bayar da agaji na kara ta’azzara musamman a yankin na arewa maso gabashin Najeriyar lamarin da ke zama barazana ga dorewar kai agajin ga al’ummar yankin.

00:48

Alhaji Abdullahi Ibrahim

Bilyaminu Yusuf

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.