Isa ga babban shafi
Najeriya

An yankewa Sojan Najeriya hukuncin kisa

Wata Kotun soji da ke zaman ta a Maidugurin arewacin Najeriya ta yankewa wani soja hukuncin kisa saboda samun sa da laifin kashe fararen hula.

Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram
Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram AFP PHOTO/SUNDAY AGHAEZE
Talla

A wata sanarwar da ta fitar, Kakakin Sojin Najeriya Kinsley Mfon Samuel, ya ce Sojan mai igiya daya John Godwin ya harbe fararen hula 5 da aka kubutar a garin Yamteke da ke jihar Borno kuma ake bincike akan su.

Sanarwar ta kuma ce akwai wasu sojoji da aka yankewa hukuncin daurin rai-da-rai kan laifukan da suka shafi kisa da samun makamai da haramtacciyar hanya.

Sojojin sun hada da Innocent Ototo mai igiya biyu da aka samu da azabtarwa tare da kisan wani yaro mai shekaru 13 da ya ce ya sace masa wayar hannu, a unguwar Zamanbari da ke Maiduguri.

Shi kuma Benjamin Osage mai igiya daya da Sunday Onwe mara igiya an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20 kan samun makamai ta haramtacciyar hanya.

Ko a watan Yuni da ya gabata an taba yankewa wani soja hukuncin kisa kan kashe wani da ake zargi dan Boko Haram ne.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Right Watch ta sha zargin Sojojin Najeriya da cin zarafin fararen hula a Rikicin Boko Haram.

HRW ta ce ana garkame da duban mutane na tsawon lokaci ba tare da hukunci ko binciken zargin da ake musu na alaka da Boko Haram ba.

Kaddamar da yakin Boko Haram ya yi sanadi rayuka akalla 20,000 daga shekara ta 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.