Isa ga babban shafi
Najeriya

Ƴan bindiga sun kai hari gidan Ibrahim Magu

Wasu ƴan bindiga sun kai hari gidan mukaddashin shugaban hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, in da suka kashe jami’in ƴan sanda guda.

Mukaddashin shugaban hukumar EFF ta Najeriya Ibrahim Magu.
Mukaddashin shugaban hukumar EFF ta Najeriya Ibrahim Magu. premiumtimesng.com
Talla

Ƴan bindigan sun kai harin ne a cikin daren da ya gabata da misalin karfe 10 a gidan Magu da ke cikin gonarsa a yankin Karshi da ke wajen babban birnin Abuja.

Wata majiya ta bayyana cewa, ɗan sanda ya mutu ne bayan tsananin dukar da ya sha daga ƴan bindigan.

Kawo yaznu babu bayani kan musabbabin harin, yayin da maharan suka yi awon gaba da shanu biyar da wasu awaki da ake kiwon su a gonar Magu.

Wannan na zuwa ne bayan wani hari da aka kai kan ofishin hukumar EFCC a cikin watan Agustan da ya gabata, abin da ya aka kara yawan jami’an tsaro don kare lafiyar Magu da iyalansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.