Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya isa Paris domin taron ɗumamar yanayi

Aƙalla shugabannin ƙasashen duniya 50 ne ake sa ran za su halarci wannan taro na birnin Paris, a daidai lokacin da aka cika shekaru biyu da ƙulla yarjejeniyar duniya kan ɗumamar yanayi wadda kasashe 195 suka sanya wa hannu.

President Buhari arrives Paris Ahead of the One Planet Summit in France on 11th Dec 2017.
President Buhari arrives Paris Ahead of the One Planet Summit in France on 11th Dec 2017. Haruna/Femi Adesina
Talla

Sai dai daga baya shugaban Amurka Donald ya janye ƙasar daga cikin waɗanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Taron na wannan talata na a matsayin yunƙuri domin cike giɓin da ficewar Amurka ta haddasa, musamman kuɗaɗen da aka yi hasashe, inda Emmanuel Macron ya sanar da ware Euro milyan 35 a matsayin gudunmuwar Faransa a asusun da aka kafa domin tunkarar wannan matsala.

Bayan sanar da ware waɗannan kuɗaɗe a cikin watan yunin da ya gabata, Macron ya roki masana da masu bincike daga kowane ɓangare, da su bayar da tasu gudumawa a wannan yunƙuri da ake yi da nufin ceto duniya daga matsalolin sauyin yanayi.

Shugaban na Najeriya zai halarcin walimar cin abincin dare da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya shirya ma shugabannin ƙasashe masu halartar taron a fadar Elysee.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.