Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya musanta ikirarin Atiku kan haramta mishi zuwa Amurka

Shugaban Najeriya Muhd Buhari musanta ikirarin tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, na cewa an haramta mishi shiga kasar Amurka tsawon shekaru 15.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar. Sahara Reporters
Talla

Cikin sanarwar da ya fitar a jiya Asabar, mai magana da Yawun shugaban Najeriyar, Mista Femi Adesina ya babu wata kasa da ta taba hana shugaba Buhari shiga cikinta bisa wasu dalilai, illa ma maraba da karbar bakuncinsa da ake a sassan duniya.

Martanin ya zo ne bayan da a jiya Asabar, wata jarida ta wallafa hirar da ta yi da Atiku Abubakar, inda ta yi masa tambayar ko mai yasa ya dauki tsawon lokaci ba tare da ziyartar Amurka, a nan ne ya bayyana cewa, ai shi kansa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, an haramta mishi shiga kasar ta Amurka tsawon shekaru 15 bisa wasu dalilai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.