Kafin yanzu dai yankin na Magumeri ya fuskanci hare-hare da ga tsagin kungiyar ta Boko Haram da ke samun goyon bayan kungiyar IS karkashin jagorancin Abu Mus’ab al-barnawi.
Ko a watan Yulin da ya gabata ma akalla mutane 69 ne da suka kunshi sojoji da sauran jami’an tsaro suka mutu a yankin bayan wani farmaki da mayakan suka kai kan kwararru masu binciken albarkatun man fetur.
A cewar kakakin runduna ta 8 ta sojin Najeriya, ko a baya mayakan sun yi yunkurin kai farmaki sansanin sojin da ke Magumeri amma sojin suka dakile yunkurin.
Wata majiyar tsaro a Maidugurin babban birnin jihar Borno, ta shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa, akwai kwakkwaran zaton cewa mayakan sun fito ne daga yankin Dabar Masara wani tsibiri a tafkin Chadi wurin da ne ake tsammanin shi ne maboyar tsagin kungiyar ta Boko Haram da ke biyayya ga Abu Mus’ab al-barnawi.