Isa ga babban shafi

Rundunar sojin Najeriya zata kafa cibiya a dajin Falgore

Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Lafatanar Janar Tukur Buratai, ya ce rundunar zata kafa katafariyar cibiya a dajin Falgore da ke karamar hukumar Doguwa a jihar Kano.

Babban Hafsan Sojan Najeriya Tukur Buratai.
Babban Hafsan Sojan Najeriya Tukur Buratai. AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Buratai ya bayyana shirin ne, yayin da ya kai wa sojojin da ke atasaye a dajin, wanda a baya ya yi kaurin suna wajen zama cibiyar ‘yan fashi, barayin shanu da kuma masu sata da garkuwa da mutane.

Babban Hafsan sojin Najeriyar, ya ce daga yanzu zasu maida dajin wajen gudanar da atasayensu na din-din-din domin murkushe miyagun da ke addabar jama’a.

A karshen shekarar 2016 da kuma farkon 2017 ne sojojin Najeriya suka kame tare da korar da dama daga cikin masu tafka ta’asa daban daban a cikin dajin na falgore bayan kaddamar da atasayen da suka yi wa lakabi da “Operation Harbin kunama”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.