Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan siyasa sun bai wa masu zabe a Anambra cin hanci

Rahotanni daga jihar Anambra da ke kudancin Najeriya na cewa, wakilan jam’iyyun siyasa mabanbanta sun yi raban abinci da kudade ga masu kada kuri’u a zaben gwamnan jihar da ake gudaarwa a yau Asabar.

An jibge jami'an 'yan sanda dubu 26 don tabbatar da tsaro a zeben na Anambra
An jibge jami'an 'yan sanda dubu 26 don tabbatar da tsaro a zeben na Anambra Reuters/Akintunde Akinleye
Talla

Premium times da ake wallafa wa a kasar ta rawaito cewa, ‘yan jaridu sun shaida yadda jam’iyyun APGA da APC da PDP suka rika raban abincin da kudin da zimmar shawo kan masu kada kuri’u.

Rahotanin na cewa, akwai wadanda aka basu Naira 500 da dubu biyu biyu a rumfunan zabe, yayin da wasu aka ba su buredin Gala da lemun kwalba na Maltina.

Ana yawan zargin jam’iyyun siyasa a Najeriya da siyan kuri’ar masu kada kuri’u musamman a ranar gudanar da zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.